Hukumar EFCC Ta Kirkiri Dakarun Mutum 7000 da Za Su Yaki Masu Tashin farashin kayan abinci
Hukumar EFCC za ta tashi tsaye, ta yaki wadanda su ke bada gudumuwa wajen karya darajar Naira Yayin da kudin Najeriya ke rasa darajarta a kasuwa,
farashin Dalar Amurka yana tashi har gobe Dakarun EFCC na musamman sun soma cafke masu cin mutuncin Naira da karbar Daloli babu dalili
A halin yanzu babu abin da Naira ta ke yi sai rasa daraja da kima a kan Dalar kasar Amurka, har su Ben Bruce sun kawo shawarwari.
Mai magana da yawun bakin hukumar EFCC a kasa, Dele Oyewale ya shaida cewa ana neman ganin yadda za a rage sululun Naira.
CBN da EFCC sun hada kai Saboda a kawo mafitar tattalin arziki, Punch ta ce ministan kudi watau Wale Edun ya yi zama da shugaban EFCC da gwamnan CBN.
Ma’aikatar tattalin arziki ta tabbatar da zaman Ola Olukoyede da Olayemi Cardoso a shafin X.












