• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Nation cup, yadda yan Najeriya ke zaman Dar-dar a kasar Africa ta kudu

aksam by aksam
February 7, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Kasashen biyu dama sun dade da jure hamayya ta tsawon shekara guda, saboda su ne ke da masana’antun nishaɗi mafiya girma a Afirka, kuma kusan su ne mafiya karfin tattalin arziki a nahiyar.

Hukumomin Najeriya a jiya Talata sun yi kira da a yi taka-tsan-tsan kan abin da suka bayyana a matsayin “barazana” ga ‘yan kasarsu da ke zaune a Afirka ta Kudu gabanin haduwar kasashen biyu a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka – wasan kwallon kafa da ke sabunta takun saka.

RelatedPosts

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Kasashen biyu dama sun dade da jure hamayya ta tsawon shekara guda, saboda su ne ke da masana’antun nishaɗi mafiya girma a Afirka, a maimakon don su na mafiya karfin tattalin arziki a nahiyar.

Sai dai a yanzu zaman dar dar na karuwa a fagen wasan kwallon kafa yayin da Najeriya da Afirka ta Kudu ke shirin buga wasan kusa da na karshe a Ivory Coast ranar Laraba.

Babban Ofishin Diflomasiyyar Najeriya a Afirka ta Kudu ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan Afirka ta Kudu na yin kalamai masu tayar da hankali a yanar gizo wadanda akasarinsu “sun kunshi barazana” ga ‘yan Najeriya.

Ofishin harkokin diflomasiyya din ya bukaci ‘yan Najeriya mazauna kasar Afrika ta Kudu da su kula da kalamansu, su lura da inda za su je kallon wasan… kuma su guji shiga cikin hayaniya, tarzoma ko tada hankali idan Super Eagles (laƙabin tawagar ‘yan wasan kwalon Najeriya) suka lashe wasan kusa da na karshen.”

Sashen hulda da kasa da kasa na Afirka ta Kudu ya ce kasar “ba ta amince da fargabar da aka bayyana ba” a cikin sanarwar, in da ta kara da cewa: “Shawarar abin takaici ne saboda da alama ta haifar da zaman dar dar tsakanin ‘yan kasar Afirka ta Kudu da ‘yan Najeriya mazauna kasar ko kuma bakin da su ka zo ziyarar Afirka ta Kudu.”

A cikin 2019, tashin hankali mai nasaba da kyamar baki a Afirka ta Kudu ya yi sanadin mutuwar mutane 12.

Najeriya da Afirka ta Kudu za su sake haduwa ne a wasan kusa da na karshe kamar yadda suka hadu a shekarar 2000, inda Najeriya ta ci da 2-0. Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a karo na uku a shekarar 2013, yayin da Afirka ta Kudu ta samu nasara a shekarar 1996.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Jam’iyun adawa sun magantu kan gazawar Tinibu da jam’iyar sa ta APC

Next Post

Ana Son Namiji Ya Riƙa Yin Jima’i Sau 21 A Wata Don Samun Tsawon Rai:- Bincike Likitoci

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano
LABARAI

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

by Abdulhamid Isa
September 7, 2026
Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Wata mata ta hadu da ajalin ta bayan Mijin ta ya daba mata wuka

Wata mata ta hadu da ajalin ta bayan Mijin ta ya daba mata wuka

October 24, 2023
Gwamna Abba Kabir ya mayar wa Ogan Boye mukaminsa tare da nada wasu mutane 8

Yadda Aka Zargin An Sace Naira Biliyan 50 Daga Asusun Gwamnatin Jihar Kano

August 12, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

September 7, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media