An kama babban ɗan’adawar nan na Kano Abdul Majid Danbilki Kwamanda tare da tasa keyarsa zuwa gidan gyaran Hali da tarbiya.
Tun da fari an gurfanar da Kwamandan ne bisa zargin yin wasu maganganu da ake zargin za su iya tunzura al’umma waɗanda suka shafi batun masarautun Kano inda Hukumar DSS ta gayyace shi tare da miƙa shi ga rundunar ƴan sanda, kamar yadda Lauyan da ke kare shi Barriser Ibrahim Abdullahi ya tabbatar wa kafar Yada labarai ta BBC Hausa.
“Ana zarginsa da yin wasu kalamai na tunzura jama’a kan batun masarautu a jihar Kano,” in ji shi.
Sai dai ya musanta zargin da ake ma sa a kotun.
Ya yi kalaman ne a wata shira da ya gabatar a wanta kafar yada labarai a Kano, bayan kalaman jagoran Kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso kan batun makomar masarautu a jihar ta Kano.
A cikin kalamansa da suka janyo kama shi, Danbilki ya ce ba za su yarda da cire sarakunan ba.
Kotu ta bayar da umarnin tafiya da shi zuwa gidan gyaran hali na Goron Dutse a Kano.
Sai a ranar 29 ga watan Janairu kotu za ta saurari buƙatar belinsa, kamar yadda lauyansa ya bayyana











