Yan sanda sun kama ‘yan fashi da masu garkuwa 14
Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Naija ta kama wasu ‘yan ta’adda 14 da suka aikata laifukan garkuwa da mutane, fashi da makami, satar mota da dai sauran laifuka,
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa daga cikin wadanda aka kama akwai Abubakar Hussaini daga kauyen Anaba, sai Buba Mohammed daga kauyen Maje da Mainasara Muhammadu na kauyen Takalafiya Ibeto-Nasko, sai kuma Ibrahim Abdullahi daga Kontagora.
Kwamishin ya ce an kama mutanen ne bisa laifin satar wani dan shekara 20 tare da karbar naira miliyan 1.6 matsayin kudin fansar sa.
A wani labarin, ‘yan bindiga sun shiga rukunin gidaje na Sagwari da ke Abuja, yankin Dutse inda suka yi awon gaba da mutane 10.
Yan bindigar sun sace mutanen ne a ranar Lahadin makon da ta gabata, kuma yi wa masu gadin rukunin gidajen dukan tsiya, kamar yadda wani ganau ya shaidawa manema labarai.










