Yayin da ake sake shiga matsin tattalin arziki, kungiyar TUC ta tura bukatu ga Shugaba Tinubu
Kungiyar ta lissafo wasu sabbin bukatu 10 ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu yayin da aka shiga sabuwar shekara
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Festus Osifo da sakatarenta, Nuhu Toro suka sanya wa hannu
The Nation ta ce an fitar jerin sabbin bukatun ne a yau Alhamis 4 ga watan Janairu.
Kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya tabbatar ya cika dukkan alkawuran da ya dauka tsakaninsa da Kungiyar Kwadago.
Sanarwar ta ce: “Daga ciki akwai biyan naira dubu 30 na rage radadi ga ma’aikatan kananan hukumomi da jihohi da kuma Gwamnatin Tarayya.
“Kuma a tabbatar an kaddamar da wannan kafin bayyana sabon mafi karancin albashi a kasar.”











