Ministan ma’adanai Dele Adeleke ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Dele Adeleke, ya ce an ɗauki wannan mataki ne sakamakon yadda kamfanonin haƙar ma’adanan ke gaza biyan kuɗaɗen da ya kamata su riƙa biya na shekara-shekara.
Ya zuwa yanzu adadin kamfanonin haƙar ma’adanai da gwamnatin ƙasar ta soke wa lasisi sun ƙaru zuwa 3,794, waɗanda suka haɗar da 619 da suka ƙi biyan kuɗaɗen, har ma da wasu guda 912 da ba sa gudanar da ayyukan su.
Ministan ya ƙara da cewa soke lasisin ba yana nufin an yafe wa kamfanonin basukan da ake binsu bane, saboda haka su kwan da sanin basukan na kansu kuma babu shakka zasu biya, domin haƙƙin ƙasa ne da ya wanzu a kansu.
Yana mai cewa tuni an riga an miƙa wa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati EFCC sunayen su domin tabbatar da ganin sun biya ko su fuskanci hukunci daidai da tanadin da dokar ƙasa ta tanada.









