Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa kasashen Larabawa ne suka shawo kansa Game da fasa harin Iran
Ya ce Babu wani jagora a ƙasashen Larabawa da jagoranci kokarin shawo kansa kada ya kai hari kan Iran, yana mai cewa ayyukan Iran ne suka sauya masa ra’ayi.
Trump ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a yayin da yake barin Fadar White House domin tafiya Florida don hutun karshen mako cewa, “Babu wanda ya shawo kaina — ni ne na shawo kaina da kaina.”
Ya kara da cewa, “Ba su rataye kowa ba. Sun soke hukuncin rataye mutanen. Wannan ya yi tasiri sosai a kaina.”












