Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kudurin kasafin kudin kasa na badi ga zauren Majalisar Dokokin ta kasa.
Ana kiyasta cewa kasafin zai ci naira tiriliyon 27, kuma sai gwamnati ta nemi rance dala biliyon daya don cike gibin
Shugaban Najeriya, zai gabatar da kudurin kasafin kudin ne a wani zama na musamman na hadin-gwiwa tsakanin `yan majalisar dattawa da majalisar wakilai.
Hon Kabiru Alhassan Rurum wanda dan majalisar wakilai ne ya shaida wa BBC cewa sun kammala shirin karbar kudurin kasafin kudin:
“Dukaninmu mun shirya tsaf domin gudanar da gagarumin wannan aiki wanda tsarin mulki kasa ya dora a kan shugaban kasa da kuma majalisun tarraya saboda haka a shirye mu ke kuma muna fatan Allah ya sa abu ya zama alheri ga kasa bakidaya” in ji shi
Kasafin kudin da yawansa ya kai naira tiriliyon 27 da doriya zai sa gwamnati ta nemi rance dala biliyan 1 don cike gibin kasafin kudin daga bankin raya kasashen Afrika.
Ta ce za a yi amfani da shi wajen aiwatar da manyan ayyuka da dawainiyar farfado da darajar naira wadda ke jin jiki a hannu dala.












