Fadar Shugaban Kasa Ta haramta fita kasashen ketare ga dukkan masu rike da maaikatu da Hukumomin Gwamnatin tarayya kuma haramcin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Afrilun 2024.
Umarnin hanin na kunshe ne cikin wata takardar mai dauke da sa hannun Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya aike wa da sakataren gwamnatin tarayya inda yace ya haramta wa jami’an gwamnatin tarayyar da suka haɗa da ministoci da shugabannin hukumomi tafiye-tafiye ƙasashen waje na wucin gadi
A wasiƙar da fadar gwamnatinsa ta aike wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume mai ɗauke da kwanan watan 12 ga watan Maris, Shugaba Tinubun ya umarce shi da ya sanar da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya matakin.
Haramcin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Afrilun 2024, kuma zai ɗauki tsawon wata uku yana aiki.
Wasiƙar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne don a rage kashe kuɗaɗen gwamnati.
Matakin Fadar Shugaban Ƙasar na zuwa ne mako uku bayan da Majalisar Zartarwa ta amince da amfani da Rahoton Steve Oronsaye na shekara 12 baya, wanda ya ba da shawarar a haɗe wasu hukumomin gwamnati don a rage kashe kuɗaɗe.












