Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta ƙasa, wato Nigeria Union of Journalists (NUJ) reshen Jihar Jigawa, ta ƙaddamar da Ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labarai na Yanar Gizo (Online Media Chapel), a wani gagarumin mataki na amincewa da inganta aikin jaridar zamani ta yanar gizo a jihar.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a Cibiyar ‘Yan Jarida ta NUJ da ke Dutse, inda aka tabbatar da Online Media Chapel a matsayin reshe na takwas da aka amince da shi a ƙarƙashin majalisar NUJ ta Jihar Jigawa.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban NUJ na Jihar Jigawa, Kwamared Isma’ila Ibrahim Dutse, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin tarihi a cikin shekaru 34 na ƙungiyar a jihar.
Ya ce kafa wannan sabon reshe na nuna aniyar ƙungiyar ta rungumar sauye-sauyen fasahar zamani tare da kare ƙa’idoji, sahihanci da ƙwarewar aikin jarida.
A cewarsa, an kafa Online Media Chapel ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin NUJ na shekarar 2022, wanda ya amince da masu aikin jaridar yanar gizo a matsayin cikakkun mambobin ƙungiyar.
Ya ce, “Wannan ƙaddamarwa ba wai kawai kafa sabon reshe ba ne, tana nuna ƙudurinmu na ƙarfafa aikin jarida na ƙwararru a duniyar da fasahar dijital ke ƙara mamaye ta, tare da kare gaskiya, daidaito, adalci, ‘yancin kai da ɗaukar alhaki.”
Dutse ya bayyana cewa a yanzu majalisar NUJ ta Jihar Jigawa tana da rassa guda takwas, waɗanda suka haɗa da Ministry of Information Chapel, Radio Jigawa Chapel, Jigawa Television (JTV) Chapel, Correspondents’ Chapel, Freedom Radio Chapel, Horizon FM Chapel, NTA Dutse Chapel da kuma sabon Online Media Chapel.
Ya ce mambobin sabon reshen za su kasance ne kawai daga kafafen yaɗa labarai na yanar gizo da aka kafa bisa ƙa’ida, masu mallaka a fili, tsarin editoci na aiki da kuma ƙwararrun ‘yan jarida da ke bin dokokin ɗabi’ar aikin jarida na NUJ.
Ya ƙara da cewa ba a kafa wannan reshe domin masu rubutun ra’ayi na kansu, masu tasiri a kafafen sada zumunta, masu ƙirƙirar abun ciki ko kuma dandamalin yanar gizo marasa ƙa’idojin aikin jarida ba.
Shugaban NUJ ya jaddada cewa duk da saurin bunƙasar aikin jarida ta yanar gizo, bai kamata ‘yan jarida su sadaukar da tantance labarai, daidaito, adalci da sahihanci saboda gaggawar yaɗa labari ba.
Ya buƙaci ‘yan jarida su yi watsi da yaɗa labaran ƙarya, bayanan da ba su da tushe, kalaman ƙiyayya da sauran ayyukan da suka saɓa wa ɗabi’ar aikin jarida, waɗanda za su iya lalata amincewar jama’a da haɗin kan ƙasa.
Ya ce yana matuƙar damuwa da yadda ake yaɗa bayanan da ba a tantance ba da kuma labarai marasa kyau a wasu dandamalin yanar gizo, yana mai cewa dole ne ƙwararrun ‘yan jarida su bambanta kansu ta hanyar bayar da rahotanni na gaskiya, inganta tattaunawa mai amfani, zaman lafiya da kuma kyakkyawan sunan jihar.
Dutse ya kuma yi kira ga duk masu aikin jarida na yanar gizo da suka cancanta da su yi rajista tare da shiga harkokin sabon reshen domin ƙarfafa ƙwarewa, ladabi da haɗin kai a sana’ar.
A wani yunƙuri na tallafa wa ‘yan jarida, ya sanar da samar da intanet kyauta a Cibiyar ‘Yan Jarida ta NUJ domin inganta bincike, ƙara yawan aiki da samar da yanayi mai kyau ga ‘yan jarida.
Ya kuma yaba wa gwamnan Jihar Jigawa, Umar A. Namadi, bisa goyon bayan gwamnatinsa ga ‘yancin ‘yan jarida, bunƙasa harkokin yaɗa labarai da kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnati da kafafen yaɗa labarai.
Haka kuma, shugaban NUJ ya yabawa Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna, Alhaji Hamisu Muhammad Gumel, saboda gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar kafa Online Media Chapel.












