Rahotanni na nuni da cewa, malaman firamare na Abuja karkashin kungiyar NUT sun shiga yajin aiki bayan gargaɗin farko da suka yi wa gwamnati.
Shugaban NUT na Abuja, Kwamared Ameh Baba, ya ce sun fara yajin aikin ne sakamakon rashin biyan su haƙƙoƙinsu da aka rike.
Kwamared Ameh Baba ya kara da cewa cikin kankanin lokaci malaman sakandare za su shiga yajin aikin don nuna goyon baya ga malaman firamare a Abuja











