Kotun ta sanya ranar ne domin saurare tare da karɓar martanin waɗanda aka yi ƙara a shari’ar wadda Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya shigar gabanta.
Mai ƙarar yana ƙalubalantar hana shi damar da doka ta ba shi a matsayinsa na babban ɗan majalisar sarki wanda majalisar dokokin Kano ta yi ta hanyar sauya dokar masarautu.











