Hukumar jindaɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON), ta bayyana cewa kamfanonin jiragen sama guda huɗu na ƙasar nan, sun buƙaci da a ƙara kuɗin hajjin bana na shekarar 2023.
Shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan, ya bayyana cewa kamfanonin jiragen sun buƙaci da a ƙara kuɗin da $250, kamar yadda rahoton Daily Trust ya tabbatar
Hukumar tace Dalilin su na neman ƙarin ya biyo bayan rikicin da ake yi a ƙasar Sudan, wanda zai sanya sai sun bi doguwar hanya kafin su isa ƙasa mai tsarki.
Da ya ke magana a birnin tarayya Abuja, wajen horar da jami’an hukumar na jihohi a ranar Asabar, din nan Hassan ya bayar da tabbacin cewa maniyyatan ba za su biya ko sisi ba a dalilin ƙarin.












