Hukumar hisbah ta yi nasarar kama wasu mutane da suke cin kasawar mushen rago da kaji hadi dayin balangunsa tare da sayar dashi ga al’umma
Kwamandan hisbah na karamar hukumar tarauni malam Nasir Adam Mai kaji yace dakarun hisbah na karamar hukumar tarauni ne sukayi nasarar kamo mutanen a daidai lokacin da suke yunkurin tafiya da naman mushen domin kaiwa kasuwa
Kwamandan yace abin da takaici yadda mutanen da suke ikirarin su musulmi need ce suna daukan mushe a bola su gyara da nufin sayar dashi ga mutane Wanda yin hakan ka iya jawo cutuka ga mutane wadanda ba za,a iya gane kansu ba don hakanne ma yayi Kira ga al’umma dasu himmatu wajen Kai mushe da suka samu na daga dabbobinsu gidan kula da namun daji ko kuma su binne shi domin kyaucewa budewa bata gari kofar siyar da naman mushe ga al’umma .
Mutanen da aka kama Aminu Abdullahi da isyaku Musa sun tabbas suna sayar da mushen ne a sabon gari kuma masu amfani da mushen sukan basu kyautar barasa tare da biyansu kudin su a gefe guda
Aminu da isyaku sun CE sunyi nadamar rungumar wannan Sana’ar da suka dauki tsawon lokaci suna gudanarwa ba tare da an kamasu ba sai a wannan karon sun kumayi al’washin dai na wannan Sana’ar kwata kwata.
Wakiliyarmu jamila sulaiman Aliyu ta labarta mana hukumar hisbar ta karamar hukumar tarauni ta umarci mutanen biyu sun binne naman duk da wani balangun mushen da sukayi duk da sun bayyana cewa Suma suncin balangun da sukayi da mushen.










