Samma da shekarau talatin (30) ke nan mutane garin Kirgi dake mazabar Haskiya a Karamar Hukumar Kubau, jihar Kaduna suke ta kirayyen gwamnatoci su kawo musu daukin gyara masu hanyar data tashi daga tsohon garin Anchau zuwa Kirgi,kwandu,famfama,wadaka har dake garin haskiya duk a karamar hukumar kubau
A cewar wani mazaunin garin Kirgi, mai suna Alhaji Yusuf Umar Kirgi yace sun kai takardu sau da dama wajan mahukunta domin a gyara musu wannan hanyar amma abin yace tura, a dan haka muna rokan gwamnatin jihar Kaduna a karkashi jagorancin Sanata Uba Sani da ta kawo musu dauki, ton da dai gwamnatin mutane karkarace











