• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Batun Dan Kanfai: Wata Jarida Ta Nemi Afuwar Gwamnatin Kano

aksam by aksam
April 26, 2026
Reading Time: 3 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

Daga Hassan Umar Gwammaja
Kamfanin yaɗa labarai na Pulse Nigeria ya fitar da sanarwar neman afuwa tare da gyara wani rahoto da ya wallafa, bayan ce-ce-ku-ce da suka biyo bayan labarin da ya danganci zargin raba ɗan kanfai ga mata a Jihar Kano.

Tun da fari, kafar yaɗa labaran ta wallafa rahoto da ke nuna cewa gwamnatin Jihar Kano ce ke da hannu wajen raba kayan, lamarin da ya haddasa suka da martani daga jama’a musamman a kafafen sada zumunta.

Sai dai daga bisani, ƙungiyar Kano Development Forum ta shiga lamarin inda ta aikewa kamfanin wasiƙa, tana neman a goge labarin tare da yin cikakken bayani domin gyara abin da ta bayyana a matsayin rahoto mai ruɗarwa.

Bayan wannan matsin lamba, Pulse Nigeria ta cire labarin daga shafinta tare da wallafa sabon bayani, inda ta amince cewa an fitar da rahoton ba tare da cikakken bincike ba, kuma bai bayyana ainihin yadda lamarin ya faru ba.

Kamfanin ya kuma bayyana cewa bai fayyace tun farko cewa gwamnatin Kano ba ce ke da alhakin abin da ya faru ba, yana mai cewa hotunan da suka yadu sun fi alaƙa da magoya bayan siyasa ne, ba wani shiri na gwamnati ba.

A cikin sanarwar neman afuwar, Pulse Nigeria ta ce yadda aka rubuta labarin ya haifar da ruɗani tare da illa ga martabar al’ummar Kano da gwamnatin jihar.

A nata ɓangaren, ƙungiyar Kano Development Forum ta yaba da gyaran rahoton, tana mai cewa hakan alama ce ta ɗaukar alhaki a aikin jarida. Ta kuma jaddada cewa gaggawar wallafa labarai ba tare da tantance gaskiya ba na iya lalata amincin kafafen yaɗa labarai.

Rahotanni sun nuna cewa ce-ce-ku-cen ya samo asali ne daga wasu hotuna da aka ɗauka yayin wani taron siyasa na jam’iyyar APC domin tarbar uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, a Kano.

Wasu mazauna jihar sun bayyana cewa lamarin ya fi nasaba da alamu na siyasa da ayyukan magoya baya, ba wani tsari na gwamnatin jihar ba.

© 2025 Kadaura 24. All Rights Reserved.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

NAHCON Ta Kaddamar da Tawagar Malamai

Next Post

Gwamnan Kano Ya Yi Allah-wadai Da Daga Dan Kamfai Da Mata Suka Yi Yayin Ziyarar Uwargidan Shugaban Ƙasa

aksam

aksam

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa  ƴar Tik-tok  Dake Unguwar  Ɗanbare A Jihar Kano
LABARAI

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

by aksam
June 20, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

by Khadija Maitaya
June 19, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

by Khadija Maitaya
June 16, 2026
China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI
LABARAI

China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI

by Khadija Maitaya
June 14, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Yan Majalisar wakilai sun bayyana dalilansu na ware wa kan su kudin siyan mototi

Yan Majalisar wakilai sun bayyana dalilansu na ware wa kan su kudin siyan mototi

October 16, 2023

Reseñando los Juegos de Lotería en Noodlespin Casino

April 22, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media