• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yan Majalisar wakilai sun bayyana dalilansu na ware wa kan su kudin siyan mototi

aksam by aksam
October 16, 2023
Reading Time: 3 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Majalisar wakilan Najeriya ta tabbatar da rahotanni da ke cewa tana shirin sayan motoci domin raba wa mambobinta.

Sai dai ta musanta cewa kuɗin kowane mota zai kai naira miliyan 200.

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

Mai magana da yawun majalisar Akin Rotimi shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce mutane na ta kambama batun sayo motocin wanda kuma ba sabon abu ba ne, a cewarsa.

Tun farko dai a cikin kwanaki da suka gabata an yi ta tafka muhawara kan cewa majalisar wakilan za ta sayo motoci, waɗanda kowace ɗaya kuɗinta ya kai kimanin naira miliyan 200 domin raba wa mambobin.

Duk da cewa mai magana da yawun majalisar bai faɗi kuɗi da kuma irin motoci da za a sayo ba, ya ce abin da take niyyar yi yana bisa tsarin doka, kuma majalisun da suka gabata ma sun yi haka.

Ya ce ko a mafi yawan lokuta “ana saya wa jami’an gwamnati a ɓangaren zartaswa daga matakin darekta zuwa sama, motoci na aiki a ofisoshinsu.”

“Abu ne mai kyau mu fito mu fayyace wa ƴan ƙasa komai. Motocin da za a saya wa ƴan majalisa za su kasance waɗanda za a yi amfani da su wajen yin ayyukansu musamman ma na kwamitocinsu. Ba motoci ne na kashin kansu ba ko kuma kyauta,” in ji sanarwar.

Majalisar ta goma, ta ce a tsawon aikin da za ta yi daga 2023 – 2027, motocin za su kasance mallakin majalisar dokoki.

“A karshen wa’adin majalisa ta goma a shekarar 2027, idan har tsarin sayar da kayan gwamnati na nan, ‘yan majalisar za su iya samun zaɓin sayen motocin daidai darajarsu a lokacin inda za su biya kuɗin a asusun gwamnati kafin su zama nasu, in ba haka ba kuma, sun zama mallakin Majalisar Dokoki ta Ƙasa.”

Al’ummar Najeriya dai na kokawa kan matsananciyar rayuwa sanadiyyar tashin farashin kayan abinci da na masarufi da ma sufuri.

Ana ɗora laifin hakan ne kan matakin cire tallafin man fetur na gwamnatin tarayyar kasar.

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta zargi gwamnatin ƙasar da laifin cire tallafin ba tare da ta ɗauki matakan kawo sassauci ga al’ummar ƙasar ba.

Bugu da ƙari akwai rashin yarda tsakanin al’umma da shugabanni, musamman ma zaɓaɓɓun ƴan siyasa a ƙasar ta Najeriya.

Sau da dama akan zargin ƴan siyasa da yin wadaƙa da kuɗaɗen gwamnati a maimakon gudanar da ayyukan da za su shafi rayuwar al’umma.

Sai dai kamar yadda majalisar ta bayyana a bayanin nata, motocin da za ta raba wa mamabobinta za su yi amfani da su ne wajen gudanar da ayyukan da suka shafi al’umma.

Majalisar wakilan ta ce tana so mutane su gane cewa manufar majalisar ta goma na tabbatar da aminci, mambobi sun kuduri aniyar ci gaba da yin aiki tukuru, musamman a batutuwan da suka shafi sanya ido, ciki har da kai wa ga wurare masu wahala a cikin ƙasar.

“Ko yaya wuri ya kasance mai wahalar kai wa, in dai har akwai ƴan Najeriya da ke rayuwa a wurin, ya zama tilas su samu wakilai da za su je su ga halin da suke ciki da tabbatar da cewa tallafin gwamnati ya kai gare su, da kuma ganin cewa an tafiyar da tsare-tsaren gwamanati yadda ya kamata,” in ji Majalisar.

Ta ce hakan zai yiwu ne kaɗai idan aka samar da motoci masu inganci da za su kai waɗannan wurare.

Haka-kuma, majalisar ta ce tana da zimmar ganin an rage yawan kuɗaɗen gudanarwa da gwamnati ke kashewa, ganin halin da ake ciki a yanzu.

Majalisar wakilan ta ce rarraba motocin da ake sa ran yi zai taimaka wajen inganta wakilci, wayar da kan al’ummar mazaɓu da kuma ayyukan sanya ido.

Ƴan Najeriya da dama sun yi Alla-wadai da batun sayawa ƴan majalisar ta wakilai motoci, musamman ma a daidai lokacin da ƙasar ke fama da tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Wasu daga cikin nasarorin da palastinawa ke samu akan yahudawan Israela

Next Post

Kalli video yadda Hamas ta harbo jiragen yaki guda tara na kasar Israel

aksam

aksam

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa  ƴar Tik-tok  Dake Unguwar  Ɗanbare A Jihar Kano
LABARAI

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

by aksam
June 20, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

by Khadija Maitaya
June 19, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

by Khadija Maitaya
June 16, 2026
China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI
LABARAI

China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI

by Khadija Maitaya
June 14, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Dalilan kamfanin KEDCO na dauke wutar lantarki na tsawon awa 12 a gobe Lahadi

Dalilan kamfanin KEDCO na dauke wutar lantarki na tsawon awa 12 a gobe Lahadi

October 28, 2023

Bezpieczeństwo i regulacje w branży hazardowej online

April 21, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media