An samu gagarumin ci gaba a tattaunawar sulhu bayan da ƙasar China ta yi alkawarin zama mai bada tabbaci cewa Amurka za ta amince da aƙalla wasu daga cikin sharuddan Iran da aka gabatar a cikin tsarin maki 10.
A matsayin nuna amincewa da ƙarfafa haɗin kai, China ta yi watsi (veto) da ƙudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya kan batun mashigin ruwa na Strait of Hormuz a yau, duk da cewa rikicin na shafar China kanta.
Majiyoyi daga kafar Middle East Spectator ne suka bayyana hakan.











