Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ta cire China a hukumance daga matsayin babbar barazanar tsaro ga Amurka.
A sabon National Defense Strategy da ake wallafawa duk bayan shekara huɗu, yanzu an bayyana cewa fifikon tsaro shi ne kare yankin cikin gida na Amurka da kuma Yankin Yammacin Duniya (Western Hemisphere).
Abin da ya janyo cece-kuce shi ne yadda Pentagon din ya kuma bayyana cewa zai bayar da tallafi “mai iyaka” ga kawayen Amurka a duniya.
Masu sharhi na cewa wannan mataki na iya haifar da illa ga makwabta da kawayen Amurka, tare da nuna damuwa kan makomar dalar Amurka da kadarorin Amurka da suka rage. Wasu kuma na kallon hakan a matsayin sabon salo na almundahanar kudi a tsarin siyasar duniya.










