Daga Hassan Umar Gwammaja
Domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen shekarar 2027.
An karɓi Abba Atiku cikin APC ne a daren Alhamis a birnin Abuja, inda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da Mataimakin Shugaban APC na Yankin Arewa maso Gabas, Mustafa Salihu, suka tarbe shi.
A jawabin da ya gabatar, Abba Atiku ya bayyana cewa ya sauya sunan ƙungiyarsa ta siyasa daga Atiku Haske Organisation, wadda ya kafa a 2022, zuwa Haske Bola Tinubu Organisation, alamar cikakken goyon bayansa ga ajandar Renewed Hope ta Shugaba Tinubu.
Ya kuma umarci dukkanin shugabanni da mambobin ƙungiyarsa da su gaggauta shiga APC, tare da fara aiki domin ganin Tinubu ya samu nasarar wa’adi na biyu a 2027.
“Na zo nan ne domin sanar da ficewata daga tsohuwar jam’iyyata, tare da shigata APC bisa tsarin shugabanci nagari da hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Sanata Barau Jibrin,” in ji Abba.
Da yake maraba da shi, Mustafa Salihu ya bayyana shigowar Abba Atiku APC a matsayin lamari mai ma’ana da nisa, yana mai cewa jam’iyyar APC ta ginu ne bisa tsari, manufofi da akida, ba son rai ko alaƙar iyali ba.
A nasa jawabin, Sanata Barau Jibrin ya yaba wa Abba Atiku bisa abin da ya kira jarumta da tsayayyen ra’ayi, yana mai cewa matashin ya yanke shawara ne bisa imani da manufofin Shugaba Tinubu, ba don sunan mahaifinsa ba.
Jam’iyyar APC dai na ci gaba da karɓar masu sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa, lamarin da ke ƙara ƙarfafa matsayinta gabanin zaɓen 2027. baya a zaɓen shekarar 2027.
An karɓi Abba Atiku cikin APC ne a daren Alhamis a birnin Abuja, inda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da Mataimakin Shugaban APC na Yankin Arewa maso Gabas, Mustafa Salihu, suka tarbe shi.
A jawabin da ya gabatar, Abba Atiku ya bayyana cewa ya sauya sunan ƙungiyarsa ta siyasa daga Atiku Haske Organisation, wadda ya kafa a 2022, zuwa Haske Bola Tinubu Organisation, alamar cikakken goyon bayansa ga ajandar Renewed Hope ta Shugaba Tinubu.
Ya kuma umarci dukkanin shugabanni da mambobin ƙungiyarsa da su gaggauta shiga APC, tare da fara aiki domin ganin Tinubu ya samu nasarar wa’adi na biyu a 2027.
“Na zo nan ne domin sanar da ficewata daga tsohuwar jam’iyyata, tare da shigata APC bisa tsarin shugabanci nagari da hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Sanata Barau Jibrin,” in ji
A nasa jawabin, Sanata Barau Jibrin ya yaba wa Abba Atiku bisa abin da ya kira jarumta da tsayayyen ra’ayi, yana mai cewa matashin ya yanke shawara ne bisa imani da manufofin Shugaba Tinubu, ba don sunan mahaifinsa ba.
- Jam’iyyar APC dai na ci gaba da karɓar masu sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa, lamarin da ke ƙara ƙarfafa matsayinta gabanin zaɓen 2027.