• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yan Majalisar wakilai sun bayyana dalilansu na ware wa kan su kudin siyan mototi

aksam by aksam
October 16, 2023
Reading Time: 3 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Majalisar wakilan Najeriya ta tabbatar da rahotanni da ke cewa tana shirin sayan motoci domin raba wa mambobinta.

Sai dai ta musanta cewa kuɗin kowane mota zai kai naira miliyan 200.

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Mai magana da yawun majalisar Akin Rotimi shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce mutane na ta kambama batun sayo motocin wanda kuma ba sabon abu ba ne, a cewarsa.

Tun farko dai a cikin kwanaki da suka gabata an yi ta tafka muhawara kan cewa majalisar wakilan za ta sayo motoci, waɗanda kowace ɗaya kuɗinta ya kai kimanin naira miliyan 200 domin raba wa mambobin.

Duk da cewa mai magana da yawun majalisar bai faɗi kuɗi da kuma irin motoci da za a sayo ba, ya ce abin da take niyyar yi yana bisa tsarin doka, kuma majalisun da suka gabata ma sun yi haka.

Ya ce ko a mafi yawan lokuta “ana saya wa jami’an gwamnati a ɓangaren zartaswa daga matakin darekta zuwa sama, motoci na aiki a ofisoshinsu.”

“Abu ne mai kyau mu fito mu fayyace wa ƴan ƙasa komai. Motocin da za a saya wa ƴan majalisa za su kasance waɗanda za a yi amfani da su wajen yin ayyukansu musamman ma na kwamitocinsu. Ba motoci ne na kashin kansu ba ko kuma kyauta,” in ji sanarwar.

Majalisar ta goma, ta ce a tsawon aikin da za ta yi daga 2023 – 2027, motocin za su kasance mallakin majalisar dokoki.

“A karshen wa’adin majalisa ta goma a shekarar 2027, idan har tsarin sayar da kayan gwamnati na nan, ‘yan majalisar za su iya samun zaɓin sayen motocin daidai darajarsu a lokacin inda za su biya kuɗin a asusun gwamnati kafin su zama nasu, in ba haka ba kuma, sun zama mallakin Majalisar Dokoki ta Ƙasa.”

Al’ummar Najeriya dai na kokawa kan matsananciyar rayuwa sanadiyyar tashin farashin kayan abinci da na masarufi da ma sufuri.

Ana ɗora laifin hakan ne kan matakin cire tallafin man fetur na gwamnatin tarayyar kasar.

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta zargi gwamnatin ƙasar da laifin cire tallafin ba tare da ta ɗauki matakan kawo sassauci ga al’ummar ƙasar ba.

Bugu da ƙari akwai rashin yarda tsakanin al’umma da shugabanni, musamman ma zaɓaɓɓun ƴan siyasa a ƙasar ta Najeriya.

Sau da dama akan zargin ƴan siyasa da yin wadaƙa da kuɗaɗen gwamnati a maimakon gudanar da ayyukan da za su shafi rayuwar al’umma.

Sai dai kamar yadda majalisar ta bayyana a bayanin nata, motocin da za ta raba wa mamabobinta za su yi amfani da su ne wajen gudanar da ayyukan da suka shafi al’umma.

Majalisar wakilan ta ce tana so mutane su gane cewa manufar majalisar ta goma na tabbatar da aminci, mambobi sun kuduri aniyar ci gaba da yin aiki tukuru, musamman a batutuwan da suka shafi sanya ido, ciki har da kai wa ga wurare masu wahala a cikin ƙasar.

“Ko yaya wuri ya kasance mai wahalar kai wa, in dai har akwai ƴan Najeriya da ke rayuwa a wurin, ya zama tilas su samu wakilai da za su je su ga halin da suke ciki da tabbatar da cewa tallafin gwamnati ya kai gare su, da kuma ganin cewa an tafiyar da tsare-tsaren gwamanati yadda ya kamata,” in ji Majalisar.

Ta ce hakan zai yiwu ne kaɗai idan aka samar da motoci masu inganci da za su kai waɗannan wurare.

Haka-kuma, majalisar ta ce tana da zimmar ganin an rage yawan kuɗaɗen gudanarwa da gwamnati ke kashewa, ganin halin da ake ciki a yanzu.

Majalisar wakilan ta ce rarraba motocin da ake sa ran yi zai taimaka wajen inganta wakilci, wayar da kan al’ummar mazaɓu da kuma ayyukan sanya ido.

Ƴan Najeriya da dama sun yi Alla-wadai da batun sayawa ƴan majalisar ta wakilai motoci, musamman ma a daidai lokacin da ƙasar ke fama da tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Wasu daga cikin nasarorin da palastinawa ke samu akan yahudawan Israela

Next Post

Kalli video yadda Hamas ta harbo jiragen yaki guda tara na kasar Israel

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Bitadakullin siyasa, an yi gidan kaso da sakataren jam’iyar PDP

Bitadakullin siyasa, an yi gidan kaso da sakataren jam’iyar PDP

February 14, 2024
Wata Kotun  A Jihar Kano Ta Tura Amarya Da Angonta Gidan Yari

Wata Kotun A Jihar Kano Ta Tura Amarya Da Angonta Gidan Yari

May 3, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media