Daga ADAMU DABO
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bawa kwamishinonisa wa’adin wata shida domin inganta ayyukan maaikatunsu
Gwamnan ya bayyana hakan ne a gidan Gwamnatin jihar Kano a yayin gudanar da Taron majalissar zartarwa Gwamnati karo na farko
Gwamna Yusuf ya ja hakalin kwamishinonisa da cewar kada su Yi Mundahana da dukiyoyin Alummar jihar Kano
Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano Adamu Dabo ya bamu labarin cewar Gwamna Yusuf ya ce duk kwamishinan da Gwamnati ta samu da Mundahanar dokiyoyin alumma nan da watanni shida masu zuwa tabbas zai bar mukaminsa
Covered/govt.House/Dabo












