Babban sufetan ƴan sanda na kasa ya ɗauki zafi kan masu yunƙurin ta da zaune tsaye da ƙone-ƙone a lokacin zanga-zangar da za a yi
IGP Kayode Egbetokun ya umarci ƴan sanda su ɗauki mataki mai tsauri kan duk wanda suka kama da aikata laifi a faɗin kasar nan
Sufetan ya bayyana cewa sun samu bayanan sirri na shirin da wasu gurɓatattu ke yi kuma ya tabbatar da cewa za su ɗauki mataki
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da IGP Kayode ya sa wa hannu da kansa gabanin fara zanga-zangar gama gari kan tsadar rayuwa a Najeriya.
Shugaban ‘yan sandan ya ce wadanda suka shirya zanga-zangar sun kasa ba ‘yan sanda cikakken bayanin kan yadda za ta gudana, a cewar Channels TV.












