Ƙungiyoyin ƙwadago ba su sauya matsaya ba kan buƙatar da suka nema na gwamnati ta biya N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi
Shugaban ƙungiyar ƙwadago na ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya bayyana cewa har yanzu suna nan kan bakansu na sai gwamnati ta biya hakan
Joe Ajaero ya bayyana hakan ne bayan shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon sun gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Villa
Da yake magana da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan kammala taro da Shugaba Tinubu, Ajaero ya ce shugabannin ƙwadagon sun je ne domin ganawa ba tattaunawa ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Shugaban na ƙungiyar ƙwadagon ya bayyana cewa za a ci gaba da taron a sati mai zuwa, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
Bayan sun gana na fiye da sa’a ɗaya, shugabannin ƙwadagon sun fito daga zaman inda suka shaidawa manema labarai cewa za su tattauna da mutanensu kafin su sake dawowa fadar shugaban ƙasan.
Shugaban ƙungiyar TUC, Festus Osifo, ya bayyana cewa sun yi wa shugaban ƙasan bayani kan matsayarsu, sannan shi ma ya yi nasa jawabin. Sai dai, bai bayyana cikakken bayani ba kan yadda zaman na su ya kasance.










