Gwamnatin jihar Borno ta yaye tubabbun ƴan Boko Haram 560 waɗanda za a mayar da su cikin al’umma bayan an gama ba su horo da koya musu sana’o’i
Wannan na cikin tsarin da gwamnatin take da shi na mayar da waɗanda suka tuba zuwa cikin al’umma, inda ya zuwa yanzu ta mayar da mutum 8,940
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya ce bincike ya nuna cewa waɗanda aka mayar cikin al’umma ba su karya doka kuma ba su komawa cikin daji
Ya ce sojoji da sauran jami’an tsaro sun tantance su tare da shugabannin gargajiya na ƙauyukansu daban-daban.
Ya ce shirin ya samu nasara kuma sun gudanar da bincike wanda ya nuna cewa wadanda aka dawo da su cikin al’umma ba su taɓa karya wata doka ba, haka kuma ba su komawa daji.
“A cikin shekaru uku da suka wuce, mun kafa tsarin ‘Borno Model’ domin mayar da tubabbun ƴan ta’adda cikin al’umma.”
“A yau muna yaye ƙarin mutum 560 waɗanda ba su da haɗari kuma yara ne ƙanana. An basu horo akan gyaran waya, kanikanci, aikin kafinta da duk wasu sana’o’i.”
Mai ba gwamnan Borno shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Abdullahi Ishaq (mai ritaya), ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun mayar da tubabbun ƴan ta’adda 8,490 waɗanda da yawa daga cikinsu ƙananan yara ne cikin al’umma.
“Mun mayar da mutum 8,490 waɗanda da yawa yara ne ƙanana. A baya mun mayar da mutum 7,930 yanzu kuma ga mutum 560, da yawa daga cikinsu ba su shekara 10 ba lokacin da ƴan ta’addan suka tafi da su da ƙarfin tsiya.”












