Wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun tare babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano, inda suka yi garkuwa da fasinjoji da dama.
Mayakan kungiyar Boko Haram sunyi garkuwa da fasinjoji a babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano.
Mayakan kungiyar Boko Haram sunyi garkuwa da fasinjoji a babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano.
Wata majiya ta shaidawa jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar cewa, da yammacin jiya Litinin ne masu tada kayar bayan suka tare hanya tsakanin Garin Kuturu da Mannanari da ke kusa da Auno, inda suka yi amfani da karfi wajen sace fasinjojin.
a cewarsu, lamarin ya tilastawa daruruwan masu ababen hawa komawa garuwan Benishek da kuma Auno don samun mafaka.
Wasu daga cikin mazauna garuruwan da fasinjojin suka nemi mafaka a cikinsu, sun shaidawa jaridar cewar basu san adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba.
Sun ce suna kyautata zaton cewa masu tada kayar bayan sun fito ne don neman kayan abinci, ganin yadda aka kansu dauke da baruka har uku.











