Babban bankin tarayya CBN ya kori ma’aikata sama da 100 cikin abin da bai gaza kwana 20.
Binciken Kafar yada labarai ta BBC ya gano yadda lamarin ya shafi sassan bankin da dama, amma ya zuwa yanzu an fara korar ne daga sashe uku.
Wadanda lamarin ya shafa yawancinsu masu manyan matsayi ne a CBN.
Yanzu mafi yawan ma’aikatan bankin cikinsu ya ɗuri ruwa saboda rashin sanin mai gobe za ta haifar.
Babu dai wanda ya yarda BBC ta naɗi muryarsa kan lamari, wasu na cewa ko hukumomin bankin ba za su iya cewa komai ba saboda rashin sanin inda aka dosa.
CBN na ci gaba da bincike kan badaƙalar da aka tafka tun daga wasu shekaru da suka wuce na baya.
Bayanai na cewa waɗannan binciken da aka yi ba su shafi ɓangaren kuɗaɗen ketare ba da sauya fasalin naira, wanda anan gaba ake tsammanin za a je kansu.











