Ibrahim Sani Gama
Shugabancin Kungiyar Kasuwar Galadima ta bayyana rashin shigowar baki siyayyar manja da man gyada zuwa cikin Kasuwar Mai ta Galadima da matsin Rayuwar da Alumma suke ciki a halin yanzu.
Shugaban Kungiyar Kasuwar Galadima Alh. Mustapha Shuibu Suleiman ne ya bayyana haka a lokacin da yake Zantawa da Manema labarai a ofishinsa dake kasuwar.
Mustapha Shuibu Suleiman yace,Alumma da dama suna cikin kuncin rayuwa,amma duk da haka mutane sun yi iya kokarinsu wajen ganin sun taimakawa marasa karfi da tallafin kayayyakin Masarufi na yau da kullum.
Shugaban Kungiyar yace,Kungiyoyin kasuwanni a jihar Kano, Sun take muhimmiyar rawa wajen taimakawa ‘Ya’yan Kungiyarsu da basu da karfi a wannan watan na Ramadana,Kasancewar lokacin ne da Alumma suke bukatar agaji da tallafi daga gurin mawadata da Gwamnatoci a matakai daban daban.
Yace, Kungiyar Kasuwar Galadima ta taimakawa marasa karfi da dama a cikin wannan watan na Ramadana domin a jika musu makoshinsu da kuma, da Dada musu da iyalansu.
Shugaban ya bayyana cewa, Kungiyar masu Sana’ar siyar da mai manja da man gyada ta jihar Kano, ba za ta gajiya ba wajen taimakawa marasa karfi da samarwa Matasa ayyukan yi domin su kasance masu dogaro da kawunansu.
Mustapha Shuibu Suleiman, ya kuma yabawa Gwamnatin jihar Kano, bisa Namijin Kokarin da take yi na tallafawa masu karamin karfi da Abincin da za su Sahur da bude baki a wannan watan na Ramadana, Musamman duba da halin matsin Rayuwa da Talakawa suka samu Kansu a ciki a fadin jihar Kano da su Kansu masu hannu da Shuni dake tsakanin Alumma.
Bugu da kari Shugaban Kungiyar Kasuwar na Galadima yayi fatan Allah yasa ayi Bukukuwan Karamar Sallah lafiya tare yin Addu’oin samun zaman lafiya da bunkasar Tattalin Arzikin Kasuwanci a fadin jihar Kano da ma Kasa baki daya.
Ibrahim sani gama











