• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kalli cikakken jawabi gameda yanke alakar soji da Niger tayi da kasar Amurka

aksam by aksam
March 21, 2024
Reading Time: 3 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Gwamnatin Nijar ta bayyana cewa zaman sojojin Amurka a kasar ya saɓa wa kundin tsarin mulkinta.

Kamar yadda jaridar trt ta kasar Turkiyya ta bayyana ta ce Dalilan da suka sa gwamnatin Nijar ta yanke huldar soji da Amurka sun kasance batutuwan da masu sharhi suka fi tattaunawa a tsakaninsu:

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

A wani gagarumin sauyin tsari, gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yanke huldar hadin gwiwa da sojojin Amurka.

Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu a shekarar 2012 ta bai wa sojojin Amurka da ma’aikatan farar hula damar yin aiki a Nijar.

Sojojin Amurka sun dade suna gudanar da ayyukansu a wani babban sansanin sojin sama a birnin Agadez mai tazarar kilomita 920 daga Yamai babban birnin kasa, inda suke amfani da wajen ta hanyar zirga-zirgar jiragen marasa matuka da ayyukan leken asiri da dai sauran su.

Wannan wuri da ake aije jiragen yaki mara matukan ya kai kimanin kudin Amurka dala miliyan 100, sannan yana dauke da sojojin Amurka 1000, sai dai sannu a hankali Nijar na ci gaba da nisanta kanta daga kasashen yamma ciki har da Faransa wacce ta mata mulkin mallaka tun bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi mata a watan Yulin bara.

Babu alamar da ke nuna cewa, kasancewar sojojin Amurka a Nijar yana taimaka wa kasar wajen shawo kan matsalolin tsaron da ta ke fama da shi, a cewar wani mai sharhi kan harkokin siyasa Malam Salissou Sa’adou da ke zama a birnin Yamai.

“Amurkawa a Nijar suna zaune ne a Agadez. Kuma Agadez na da tazara mai yawa daga Tilleberi da Diffa inda ake gwabza fada da ‘yan ta’adda da masu tsattsauran ra’ayi. Don haka, ban ga wata matsala ba wajen neman su fice daga kasar,” kamar Sa’adou ya shaida wa TRT Afrika.

Sanarwar da Nijar ta fitar kan yanke huldar sojojinta da na Amurka na zuwa ne bayan da tawagar sojojin Amurka da ta diflomasiyya suka bar kasar bayan wata ziyarar kwanaki uku da suka kai ba tare da ganin shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tiani ba.

Mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka a Afirka, Molly Phee da kwamandan rundunar Amurka a Afirka, Janar Michael Langley na daga cikin tawagar.

Kakakin gwamnatin mulkin sojin Nijar Kanar Amadou Abdramane ne ya sanar da kawo karshen yarjejeniyar sojin Nijar da Amurka ta gidan talabijin din kasar.

Ya ce kasancewar jami’an Amurka a Nijar ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, kamar yadda ya ce an sanya shi ne ba tare da izini ba a shekarar 2012.

Ya kuma kara da cewa tawagar Amurka ba ta bi ka’idojin diflomasiyya ba a ziyarar da ta kai kasar, kasancewar ba a sanar da Nijar wadanda za su zo ba da kuma ranar zuwansu da ajandarsu ba.

“Gwamnatin Nijar ta yi soki matakin tare da yin Allah wadai kan halin rashin da’a da kuma barazanar daukar fansa da shugaban tawagar Amurkar ya yi kan gwamnati da al’ummar Nijar,” in ji Kanar Abdramane, yana mai karanta sanarwar a hukumance ta gidan talebijin din kasar.

Dangantaka tsakanin kasashen ya yi tsami ne tun bayan da gwamnatin Amurka ta bayyana karbe ikon mulki a kasar a matsayin matakin juyin mulki a watan Oktoban 2023.

Duk da wannan matakin da Nijar ta dauka, Molly Phee ta ce Amurka za ta iya ci gaba da baiwa kasar tallafin soji. Sai dai kuma Amurkan ta nuna damuwarta kan yadda Nijar ke kara kulla alaka da Rasha.

Kara nuna kyama ga kasashen yammacin duniya

Ana dai kallon wannan sabon ci gaba da aka samu a Nijar a matsayin wata alama ta nuna kyama ga kasashen yammacin duniya da ke kara ruruwa a yankin Sahel na Afirka biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashe da dama da suka hada da Nijar da Mali da Burkina Faso.

Rundunar sojin Nijar ta fatattaki sojojin Faransa daga kasar a bara, bayan shekaru biyu da Mali ta fitar da su ita daga kasar.

Kimanin sojojin Faransa 1,500 ne suka janye aikinsu daga kasar a watan Janairu, bayan zanga-zangar tsawon wasu makonni da ƴan Nijar suka kwashe suna yi.

Mai sharhin ya yi imanin cewa matakin na Nijar da ta dauka ba zai yi wani tasiri babba ba kan yanayin tsaro a yankin sahel inda kungiyoyi daban-daban masu dauke da makamai ke kai munanan hare-hare a ‘yan shekarun nan.

“Wannan ci gaban zai karfafa kudurin kasashen Sahel na hadin gwiwa don tabbatar da cewa sun fuskanci matsalar rashin tsaro.” in ji shi.

Sai dai Sa’adou ya ce dole ne gwamnatin mulkin sojin Nijar ta kara zage damtse wajen tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan kasar domin tabbatar irin goyon bayan da jama’ar suka bayar ga matakin da ta dauka na inganta ‘yancin kasar.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

FG ta fara kama sunayen mutane 15 da suke daukar nauyin taaddanci a Najeriya

Next Post

Shugaba Tinubu ya dauki tsatstsauran mataki akan ministoti da sauran mukarraban gwamnatinsa

aksam

aksam

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa  ƴar Tik-tok  Dake Unguwar  Ɗanbare A Jihar Kano
LABARAI

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

by aksam
June 20, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

by Khadija Maitaya
June 19, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

by Khadija Maitaya
June 16, 2026
China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI
LABARAI

China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI

by Khadija Maitaya
June 14, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

An Yi Aringama Tsakanin Rudunar  ‘Yan Sanda Ta Kasa Da ‘Yan Uwa Almajiran  El- Zakzaky A Abuja

An Yi Aringama Tsakanin Rudunar ‘Yan Sanda Ta Kasa Da ‘Yan Uwa Almajiran El- Zakzaky A Abuja

August 26, 2024
Bayan kai hari garin Kahutu Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

Fitaccen mawakin siyasa Rarara Ya Nêmi afuwar Yan Arewa 

July 30, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media