Osita Okechukwu yana da ra’ayin da ya sha bam-bam da na kungiyoyin kwadago da ‘yankasuwa
‘Dan siyasar da yana cikin jagorori a APC ya ce bai kamata a laftawa ma’aikata albashi a irin yanzu ba
Tsoron Okechukwu shi ne karin albashin zai jawo tashin farashi bayan yadda ake kukan tsadar kaya
Tsohon shugaban na hukumar VON ya tuna da kuskuren da ya ce kwamitin Jerome Udoji ya yi a mulkin Yakubu Gowon a 1972.
Jerome Udoji ya bada shawarar ayi wa ma’aikata karin albashi a lokacin da aka samu kudi, a karshe hakan ya jawo matsala.
Wasu suna ganin daukar shawarar Udoji da gwamnatin soja tayi ya haifar da hauhawar farashi wanda ana kuka da shi har yau.
“Ra’ayin da na dauka shi ne shakka-babu, yin kari mara tsari zai jagwagwala matsalar hauhawar farashin da mu ke da shi a kasar.”











