• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Jam’iyun adawa sun magantu kan gazawar Tinibu da jam’iyar sa ta APC

aksam by aksam
February 7, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Jam’iyyun adawa sun mayar da martani, kan zarginsu da APC ta yi na cewa suna da hannu wajen tunzura jama’a domin yi wa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bore.

Lamarin ya biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar a jihohin Kano, da Neja da Legas, kan tsadar rayuwa.

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

Sai dai a cewar jam’iyyun adawar jama’iyyar APC ce a kan mulki, don haka alhakin tabarbarewar lamurra a kasar ya rataya ne a wuyanta.

Manyan jam’iyyun adawar Najeriya PDP da LP, sun ce cunar rigar jam’iyyar APC ce ke neman kayar da ita, kuma tun farko kankanba ce ta kai ta ga neman sahalewar ‘yan Najeriya domin jagorantarsu, ba tare da wani tartibin tsarin yaye musu matsalolin da suke ciki ba.

Shi ya sa a yanzu bayan shafe kusan shekara guda a kan Mulki da shugaba Tinubu ya yi, take zarginsu da yi wa gwamnati shune, kamar yadda jam’iyyun biyu suka bayyana.

Mataimakin kakakin babbar jam’iyyar adawa ra Najeriya PDP na kasa Malam Ibahim Abdullahi, ya ce ” APC ta sauka ta ba su mulkin ta koma tana zuga da tunzura al’umma idan tana ganin hakan shi ne daidai.”

“Talaka na ciki halin ha’ula’i na mummunan rashin tsaro, da ƙangi na talauci da ƙunci na rashin inda zai saka gaba, amma a ce bai da ikon ya fito ya faɗi halin da yake ciki, sai gwamnati ta zargi jam’iyyun adawa, wannan rainin wayau ne a buge ka kuma a ahanaka kuka,” in ji Malam Ibrahim.

A cewarsa. ” kowa a Najeriya ya san halin da ake ciki, a gwamnatance APC ta gaza gaza, ba su iya ba.”

Irin wannan martani ne ita ma jam’iyyar adawa ta Labour ta mayar, tana mai nuni da cewa kamata ya yi APC ta zargi kanta, ba wai zargin ƴan’adwa ba

Kakakin jam’iyar LP na ƙasa Dr Tanko Yunusa ya ce ” Su ne da kan su suka tunzura mutane saboda sun yi wa al’umma ƙwace, sun saka su cikin yunwa, sannan an hana su magana, kun hana su zuwa makarantu, kun ce kada su je gona saboda riƙon sakainar kashi da suka yi wa mutane.”

Dr Tanko ya ce da gwamnati ta yi abin da ya dace da ba a samu matsalar da ake fuskanta ba.

“Yanzu dala ta kai 1,500 , yanzu mu ne muka yi haka? mu ne a gwamnati ? kuma su ma ƴan Najeriya wayayyi ne, ko ana nufin ba su san ƴancin kansu ba? sun nuna sun gaza, saboda da mulkin Buhari da na Tinubu kamar Ɗanjuma ne da ɗanjummai,” in ji Dr Tanko.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Wani gwamna a Arewa ya dauki matakin rage kudin man fetur ga Manoma

Next Post

Nation cup, yadda yan Najeriya ke zaman Dar-dar a kasar Africa ta kudu

aksam

aksam

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa  ƴar Tik-tok  Dake Unguwar  Ɗanbare A Jihar Kano
LABARAI

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

by aksam
June 20, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

by Khadija Maitaya
June 19, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

by Khadija Maitaya
June 16, 2026
China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI
LABARAI

China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI

by Khadija Maitaya
June 14, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Analyse approfondie de l’économie du gaming : l’essor des machines à sous en ligne

April 21, 2025
Ƙarancin Abinci, Hedkwatar Tsaro ta tura rundunar soji ta bawa manoma kariya a wasu jihohin Arewa

Ƙarancin Abinci, Hedkwatar Tsaro ta tura rundunar soji ta bawa manoma kariya a wasu jihohin Arewa

August 15, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media