DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Gwamnatin tace ta dakatar da amincewa da takardun shaidar kammala jami’o’in kasashen Benin da Togo, a kasar nan.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Augustina Obilor-Duru, ya fitar a madadin Daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi ta tarayya.
Dakatarwar ta biyo bayan wani rahoton binciken kwa-kwaf da jaridar Daily Nigerian ta gabatar mai take “Yadda wakilin jaridar DAILY NIGERIAN ya samu digirin daga Cotonou a cikin sati 6”.
Sanarwar ta ce, yanzu haka za’a ci gaba da jiran sakamakon bincike daga ma’aikatun harkokin waje da ilimi na kasar nan da kuma na kasashen biyu har ma da hukumar tsaron farin kaya DSS, da kuma hukumar kula da masu yi wa kasa hidima.











