Shugaban jam’iyyar APC, Dakta Abdullah Umar Ganduje ya soki jigon jam’iyyar a Najeriya, Salihu Lukman.
Lukman wanda tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ce a Arewa maso Yamma ya sha sukar tsare-tsaren jam’iyyar.
Ganduje ya bayyana Lukman a matsayin dan siyasa wanda ba shi da mafadi da kuma rashin sanin inda ya dosa, cewar Legit.ng
Hadimin shugaban a bangaren wayar da kan jama’a, Cif Oliver Okpala shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Litinin 1 ga watan Janairu.
Okpala ya yi martani ne bayan Lukman ya kwatanta Ganduje da cewa ya na shugabanci irin na tsohon shugaban jam’iyyar, Abdullah Adamu.












