Shugabancin kungiyar tsofaffin daliban kwalejin kimiyya da fasaha ya Bagauda Dake dakatsalle dake Nan jihar Kano ya yabawa injiniya Abba Kabir Yusuf bisa yadda yayi alkawarin dawo da martabar kwalejin duba da yadda ta lalace..
Shugaban kungiyar injiniya Mustafa Hassan ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Nan jihar Kano.
Injiniya yace ‘ya’yan kungiyar tsofaffin daliban kwalejin ne suka Rika daukar wasu nauye nauye da dama na kwalejin domin ganin komai ya daidaita tun lokacin da aka kulle makarantar saboda matsalar rashin tsaro da yayi sanadin kulleta.
Yace, Amma yanzu ga shi Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf ya tura domin duba makarantar tare da zo masa da rahoton abubuwan da aka gani domin gyrawa,inda yace kungiyar tsofaffin daliban kwalejin ba za su taba mantawa da shi ba saboda yadda yake da mayar da hankali akan harkoki da dama ciki har da ilimi.
Shugaban kungiyar tsofaffin Daliban makarantar kwalejin Bagauda injiniya Mustafa Hassan ya bayyana cewar, duba da irin gudunmawar da kwalejin Bagauda take yi da irin Mayan injiniyoyin da ta yaye a shekarun da suka gabata ya Sanya Gwamntin jihar Kano ta tura da wakilai domin zuwa kwalejin Bagauda tare kawo cikakkun rahotanni akan irin gyara gyaran da za a yi mata saboda kulawa da harkokin ilimi da Gwamnti Mai ci take shi.
Injiniya Mustafa yace babu abin da za su cewa da maigirma Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake da sha’awar ganin ilimin jihar Kano ya inganta kamar sauran Jihohin da suka Yi fice a najeriya.
Shugaban kungiyar tsofaffin Daliban kwalejin ta Bagauda injiniya Mustafa yayi kira ga sauran Gwamnonin Jihohin kasar Nan da su yi koyi da irin halayen Gwamnan jihar Kano na bunkasa fannin ilimi.
Daga karshe ya shawarci ‘ya’yan kungiyar tsofaffin Daliban kwalejin Bagauda da su ci gaba da marawa yunkurin Gwamntin jihar Kano baya da Kuma ita kanta kungiyar domin an ciyar da kwalejin Bagauda dake dakatsalle a Nan jihar Kano.











