Daga Hassan Umar Gwammaja
Wannan hukunci ya jawo suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ƴan jarida, waɗanda suka bayyana shi a matsayin rashin adalci.
An kama Cumpio mai shekaru 26 ne a watan Fabrairun 2020, bayan da sojoji suka kai farmaki gidanta da tsakar dare, inda suka ce sun samu gurneti, bindiga da kuma tutar ƴan gurguzu.
Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun musanta tuhume-tuhumen, suna mai cewa an kama ta ne saboda sukar jami’an tsaro.
Bayan shafe kusan shekara shida a tsare ba tare da shari’a ba, kotu ta wanke ta daga zargin mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, amma ta same ta da laifin tallafa wa ta’addanci. Masu lura da al’amura sun danganta lamarin da ƙara take haƙƙin ƴan jarida a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar, Rodrigo Duterte.












