Daga: Hassan Umar Gwammaja
A kwanakin da suka gabata ne dai rundunar ta gayyaci sarkin domin bayar da bahasi kan abin da ya faru ranar Idin ƙaramar sallah lokacin da sarkin ke komawa gida a kan doki bayan kammala sallar Idi, inda wasu matasa suka far wa tawagarsa har suka halaka ɗaya daga cikin masu ba shi kariya..
To sai dai cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce ta janye gayyatar bisa shawarar wasu mutane da ƴansandan suka kira ”masu ruwa da tsaki da take kimantawa”.
Haka kuma ƴansanda sun ce daga cikin dalilan janye gayyatar har da muradin babban sifeto ƴansandan na tabbatar da cewa ba a siyasantar da aikin ƴansanda ba ko yi wa aikin mummunar fahimta.
”A maimakon haka babban fifeton ƴansandan ya aike da wata tawagar rundunar ta sashen tattara bayanan sirri da su je fadar sarkin domin jin bahasinsa kan abin da ya farun”, in ji sanarwar.
Gabanin bukukuwan ƙaramar sallah ne dai rundunar ƴansanda reshen jihar Kano ta fitar da sanarwar hana Hawan Salla, saboda bayan da ta ce ta samu na sirri da ke nuna cewa za a iya samun tashin hankali.











