Daga: Hassan Umar Gwammaja
An haife shi a ranar 8 ga Nuwamba, 1938 a Kano. Ya kasance sojan Najeriya kuma Shugaban Ƙasa na mulkin soja daga 1975 zuwa 1976.Ya karɓi mulki ne bayan hambarar da Janar Yakubu Gowon. Gwamnatinsa ta shahara wajen tsauraran matakai na gyaran gwamnati, yaƙi da cin hanci da rashawa, da kuma ƙarfafa ɗa’a a ma’aikatan gwamnati.
Murtala Muhammad ya yi suna da jarumtaka, gaskiya da adalci, lamarin da ya sa al’umma suka ƙaunace shi matuƙa. Sai dai a ranar 13 ga Fabrairu, 1976, aka kashe shi a juyin mulki a Legas, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa ofis.
Mutuwarsa ta girgiza Najeriya ƙwarai, kuma har yau ana tunawa da shi a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin da suka fi tasiri a tarihin ƙasar nan.












