Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin kare dimokuraɗiyya da martabar ƙasa. Gwamnatin ta bayyana cewa wannan haɗin gwiwa yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da inganta fahimtar jama’a kan al’amuran gwamnati da tsaro.
Da yake jawabi a taron ƙasa na tsaro na ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke gudana a Abuja, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya isar da saƙon Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf. Ya bayyana muhimmiyar rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen gina ra’ayin jama’a da tallafa wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa kafafen yaɗa labarai su ne hanya mafi tasiri wajen isar da manufofin gwamnati ga matasa da sauran al’umma. Ya kuma ce ya rataya a wuyan ‘yan jarida su taimaka wajen yaƙi da labaran ƙarya, yaɗa bayanan da ba su da tushe, da kuma ɓatar da jama’a ta hanyar bayanan ƙarya. A cewarsa, wannan wani ɓangare ne na nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora wa ‘yan ƙasa domin kare martabar ƙasa.
Haka kuma, Waiya ya yaba da taken taron wanda ya mayar da hankali kan alaƙar da ke tsakanin tsaro da ayyukan kafafen yaɗa labarai, yana mai cewa lokaci ya yi da ya dace kuma yana da hangen nesa. Ya ƙara da cewa rahotannin da suka shafi tsaro na buƙatar kulawa ta musamman, inda ya kamata kafafen yaɗa labarai su daidaita tsakanin ‘yancin aikin jarida da kuma kare muradun ƙasa. Ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da kyakkyawar alaƙa da hukumomin tsaro, tare da ba su tallafi na motoci da kayan aiki ga rundunar ‘yan sanda, NSCDC, JTF da sauran hukumomin tsaro domin sauƙaƙa ayyukansu.












