Daga Hassan Umar Gwammaja
Dr. Tahar Adamu Baba, wanda aka fi sani da “Impossible”, ya bayyana cewa neman mafaka da kuma samun abin kashewa ne ya sa Malam Ibrahim Shekarau komawa jam’iyyar APC
Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar Lumana Radio.
Dr. Tahar ya ce komawar Shekarau APC ba ta rasa nasaba da yanayin siyasa da kuma bukatar samun mafita a halin da yake ciki.
Sai dai bai yi karin bayani dalla-dalla ba kan wasu dalilai na daban da ka iya haddasa sauyin tafiyar siyasar tsohon gwamnan.












