• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kashi Bakwai Cikin Dari Na Kudin Sayen Makamai Kacal Aka Damka Wa Sojoji A 2025 :— Rahotanni

aksam by aksam
April 20, 2026
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
465
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Hassan Umar Gwammaja

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

A Wani alƙaluman da gwamnatin tarraya ta fitar sun nuna kashi 7 cikin 100 kacal na kasafin kuɗin da aka ware domin sayen makamai kawai aka damƙa wa Rundunar Sojin Ƙasa na Najeriya.

Daga cikin Naira biliyan 34.71 da aka ware wa gyaran jiragen yaƙi na Rundunar Sojin Sama, Naira biliyan 4.85 kacal (kashi 13.98%) aka fitar. Ba a saki ko sisi ba domin man motocin sufuri da na jiragen sama da ɗaukar ma’aikata da gina barikin soja da bincike da bunƙasa aiki.

Daga cikin Naira biliyan 15.75 da aka ware wa sayen kayan tsaro na Rundunar, an saki Naira biliyan 5.25 (kashi 33.33%). Amma sayen kayan kare ƙasa ya samu koma baya sosai, inda aka saki Naira biliyan 19.25 kacal (kashi 6.45%) daga cikin Naira biliyan 298.44 da aka ware.

Kasafin Naira biliyan 117.90 na gyaran kayan tsaro ya samu kashi 3.99% (Naira biliyan 4.71), amma ba a saki ko sisi ba domin ginawa da samar da kayan tsaro (Naira biliyan 7.16). Kula da jin daɗin sojoji (Naira miliyan 28.33) bai samu ko sisi ba, haka ma gina barikin soja (Naira miliyan 95.68), gyaran barikin soja (Naira biliyan 6.76) da kuɗin mai na wasu motocin sufuri (Naira miliyan 45.03), duk ba su samu ko sisi ba.

Sauran muhimman abubuwa da suka samu ƙarancin kulawa sun haɗa da kuɗin mai na jiragen sama (Naira biliyan 2.23 daga cikin Naira biliyan 43.91 – kashi 5.07%), kudin mai na motocin aiki (Naira biliyan 1.71 daga cikin Naira biliyan 4.41 – kashi 38.72%) da horon kasashen waje (Naira biliyan 2.20 daga cikin Naira biliyan 17.56 – kashi 12.50%).

Sai dai horon cikin gida, gyaran motocin aiki, hidimar tsaro da kuɗin tsaro sun samu aiwatarwa mai gwaɓi da kashi 41.56%, 58.28%, 98.10% da 79.65% bi da bi.

Ƙoƙarin da aka yi jiya wajen jin ta bakin rundunar tsaro kan aiwatar da kasafin bai yi nasara ba, domin kira da aka yi wa Daraktan Hulɗar Soja, Birgediya Janar Samaila Uba, bai ɗauka ba, kuma bai amsa rubutattun sakonnin tes da na WhatsApp da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Share186Tweet116SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Ku Daina Kukan Talauci, Najeriya Ba ƙasa ce Matalauciya ba; — Fadar Shugaban Ƙasa

Next Post

Babbar Kotun Tarayya Dake Zamanta Abuja; Karƙashin Mai Shariʼa Peter Odo Lifu Ta Bayar Da Umarnin A Sakin Sheikh Sani Khalifa Zaria Ba Tare Da Bata Lokaci Ba

aksam

aksam

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa  ƴar Tik-tok  Dake Unguwar  Ɗanbare A Jihar Kano
LABARAI

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

by aksam
June 20, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

by Khadija Maitaya
June 19, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

by Khadija Maitaya
June 16, 2026
China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI
LABARAI

China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI

by Khadija Maitaya
June 14, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Wata Kotu A Jihar Kano Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Daurin Watanni Biyu Bisa Sare Bishiyu Ba Akan Ka’ida Ba

Wata Kotu A Jihar Kano Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Daurin Watanni Biyu Bisa Sare Bishiyu Ba Akan Ka’ida Ba

April 26, 2025
Tsohon shugaban Majalisar tarayya ya fadi yawan albashi da alawus dinsa da nufin wanke kansa

Tsohon shugaban Majalisar tarayya ya fadi yawan albashi da alawus dinsa da nufin wanke kansa

July 3, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media