Hukumar kula da yanayin saukar ruwan Sama tsawa ta kasa NiMet ta yi hasashen yawaitar tsawa a ranakun Litinin, Talata da Laraba a sassan Najeriya daban-daban
Hukumar ta fitar da hasashen ne a yammacin jiya a babban birnin tarayya Abuja.
Ta ce jihohin da tsawar zata shafa daga Arewacin Najeriya sun hadar da Borno, da Yobe, da Jigawa, da Taraba, da Adamawa, da Gombe, da Bauchi, da Kano, da Katsina, da Kaduna, da Zamfara, da Kebbi da kuma Sokoto
A bangaren kudu maso yamma jihohin da abin zai shafa sun Hadar da Oyo, da Ondo, da Osun, da Ekiti da Ogun da kuma jihar Lagos.
Sai kudu maso kudu da kudu maso Gabas da tsawar zata shafi jihohin Delta, da Rivers, da Cross River, da Akwa Ibom da Bayelsa da Enugu, da Edo, da kuma Ebonyi












