Daga Abubakar Suleiman Gwammaja
Wasu daga cikin masu sauraron tashar FRCN ta Kaduna sun magantu sakamakon rashin gudanar da shirye-shirye na tsawon sati hudu da tashar Bata yi
A zanrawar sa da jaridar online rta Solacebase daya daga cikin masu koken mai suna Musa Ibrahim mazaunin Karamar Hukumar Ikara yace basa Jin dadin rashin yada shirye-shiryen tashar kasancewar suna amfana da shirye-shiryen ta ake yada wa a tashar
Kazalika wani mai suna Hassan tashar yari ya ce basa Jin dadin yanayin da tashar ta Sami kanta kasancewar basu taba shiga irin wannan mummunan yanayin ba fiye da shekara 10
Kana ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakan da suka dace domin tsamo tashar daga mummunan yana yin da take ciki.












