Duk da irin tarin takunkumi da aka kakaba wa Rasha bayan mamayar da ta yi a Ukraine, ƙasar ta bai wa masana tattalin arziki da dama mamaki ta hanyar zama ƙasar da tattalin arzikinta ke haɓaka cikin sauri a Turai.
“Tattalin arzikin na cikin yanayi mai kyau, dukkan abubuwa na tafiya yadda ya kamata, kuma hakan ya saka Putin zama sananne saboda ya sake nuna kansa a matsayin mutumin da ya bijire wa Yamma kan takunkumi da suka saka wa tattalin arzikin Rasha,” in ji wakilin BBC a ɓangaren kasuwanci, Alexey Kalmykov.
Maimakon faɗuwa ƙasa kamar yadda mutane da dama suka yi tsammani, tattalin arzikin Rasha ya ƙaru da kashi 2.6, a cewar kiyasin Hukumar Ba Da Lamuni ta Duniya (IMF), duk da takunkuman Yamma, da suka haɗa da hana Rashar taɓa kuɗinta da ya kai $300b.
Sai dai waɗannan takunkumai ba su yi aiki a faɗin duniya ba. Wannan ya bai wa Rasha damar hulɗar kasuwanci da ƙasashen China, Indiya da kuma Brazil yayin da makwabta, ciki har da Kazakhstan da Armenia, na taimaka wa Rasha kauce wa takunkuman Yamma.
“Tattalin arzikin Rasha na da grima,” in ji Kalmykov, ya ƙara da cewa: “Za a ɗauki tsawon gomman shekaru kafin takunkumai ko ɓarnar kuɗi su kai tattalin arzikin Rasha ƙasa amm dai ba yanzu ba.”
“Rasha na samun kuɗi ta hanyar fitar da kayyaki waje kuma tana da damar sayar da duk abin da take so,” a cewar Kalmykov. “takunkumi kan man fetur na je ka nayi ka one, sai dai babu takunkumi kan iskar gas da kuma nukiliya daga Tarayyar Turai saboda suna cikin waɗanda ke sayen abubuwan daga Rasha.”
Dr Schulmann ya ce duk da cewa farashin kayyaki ya ninka har sau huɗu ba kamar a baya ba, a shirye suke, wanda ta ce yana da muhimmancin gaske.
“An san Rasha da ƙara farashin kayayyaki. Fargabar da muke da ita ba wai ta hauhawar farashi ba ne, sai dai illa giɓi.
Kalmykov ya amince cewa: “Abu ɗaya shi ne farfagandar Putin na iya yin tasiri matuka.”










