Shugaban ya naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON).
A wata sanarwar da fadar Shugaban Ƙasa ta fitar mai dauke da sa hannun Mai magana da yawun shugaban Kasa Bayo Onanuga, ya ce naɗin na jiran amincewar Majalisar Dattawa, kamar yadda sashe na 3(2) na dokar NAHCON ta shekarar 2006 ya tanada.
Shugaba Tinubu ya aike da wasiƙa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, inda ya buƙaci a gaggauta tantancewa da amincewa da naɗin Ambasada Yusuf domin maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a wannan mako bayan shafe kusan watanni 14 a kan muƙamin.
Ambasada Ismail Abba Yusuf ƙwararren jami’in diflomasiyya ne na Najeriya, wanda ya taɓa zama Jakadan Najeriya a kasar Türkiye daga shekarar 2021 zuwa 2024.












