Kungiyar masu sana’ar kasuwancin katifu na jihar Kano sun bayyana rashin shigowar baki daga wasu jihohin kasar Nan da cewa, tsadar takin zamani ne da rashin tsaro da ake samu a wasu yankunan kasa baki daya.
Sakatare kungiyar Alh Ibrahim Wanda Alh Nasuru Abdulrahaman ya wakilta ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake kasuwar.
Yace kamata yayi Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf ya Kara kwazo da mayar da hankali akan batun harkokin tsaro saboda rashin tsaro ba karamin matsalar bace. akan noma,. inda yace wasu manoma ba sa samun daman yin Nomansu saboda gudun kar a hallakasu a yankunan Arewacin kasar Nan Wanda wasu ma sun hakura noma, musamman a. Katsina da zamfara da Maiduguri da sokoto.
Nasuru Abdulrahaman ya bayyana cewa Kungiyoyin masu garkuwa a yankunan Katsina sun ta matsowa, a don haka mutane suka rage zuwa siyayya a lokaci irin wannana na kaka Wanda da yawa manoma sai sun siyar da kayan amfanin gonane suke samun kudade da za su shigo kasuwanni domin yin siyayyar kayayyakin da suke bukata.
Nasuru Abdulrahaman yace hatta masu Saka bukukuwan Auren ‘ya’yan su sun fi sakawa a lokutan kaka saboda a wannan lokacin ne suke samun kudade inda yace to noman ma Basu samu damar Yi ba balantana su zo su yi siyayyar kayayyakin da suka Saba.
A don haka ya yake kira ga Gwamnatin tarayya Dana jihohin Arewacin kasar Nan, da su duk maiyiyuwa domin ganin sun dakile matsalolin rashin tsaro a yankunan da suke fama da wadan Nan matsaloli na rashin tsaro saboda matsalar ta shafi bangarori da dama na kasar Nan.
Haka zalika, Alh. Nasuru Abdulrahaman yace, tsadar da takin zamani yayi ya taka muhimmiyar rawa wajen Hana mutanen da suke shigowa cikin jihar Kano domin yin siyayyar kayayyakin da suke bukata don yin amfani da shi a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.

Yace akwai bukatar Gwamnatin tarayya ta karya farashin takin zamani Wanda a cikin Kashi dari na mutanen da suke a Arewacin kasar Nan wannan tsadar takin ta shafe su, inda ya shawarci dukkanin Gwamnatoci da masu ruwa da tsaki na kasa baki daya,da su taimakawa alumma wajen rage farashin takin zamani da manoma suke siya don amfani da shi.
Daga karshe ya yabawa alummar kasuwar masu hada Hadar kasuwancin katifu ta hanyar IBB da sauran yankungiyar masu sana’ar katifu musamman jagororin kasuwar bisa yadda suke ba da gudunmawa wajen ci gaban kasuwancin alumma da kare martabarsu.
Ibrahim sani Gama radio Nigeria pyramid











