A alamu kasar Tehran na shirin fuskantar sabuwar takaddama maimakon zaman lafiya, bisa ga kalaman da Jagoran Musulmin kasar Ayatollah Ali Khamenei ya yi kwanan nan.
Khamenei ya bayyana ra’ayi mai nuna cewa Iran ta fi son shiga cikin rashin tabbas na rikici da Amurka, fiye da amincewa da bukatun sulhu da ake ganin suna kaskantar da martabar ƙasar.
Kalaman Khamenei sun zo ne a lokacin da ake ci gaba da takaddama tsakanin Tehran da Washington kan batutuwan shirin makamashin nukiliya, tallafin Iran ga kungiyoyin da Amurka ke kallo a matsayin masu tayar da hankali, da kuma matsin lambar da ake yi don rage tasirin Iran a Gabas ta Tsakiya. Masana na ganin cewa wannan sabon yanayi na iya kara dagula al’amura a yankin, inda Iran ke nuna cewa za ta kare kanta daga duk wata barazana ta kasashen yamma











