Jihar Plateau – Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya shiga zanga-zangar da matasa ke yi a birnin Jos na jihar Plateau.
Tsohon ministan ya shiga zanga-zangar ne wacce ake gudanarwa kan halin ƙunci da wahalar da ake fama da ita a ƙasar nan.
Masu zanga-zangar lumanan sun riƙe alluna da kwalaye waɗanda aka yi rubuce-rubucen kira ga gwamnati na ta tashi tsaye ta yi abin da ya dace.
Tsohon ministan ya yi jawabi ga matasan da suka fito domin nuna adawarsu da halin ƙunci da yunwar da ake fama da ita a ƙasar nan, cewar rahotom jaridar New Telegraph.
Dalung ya buƙaci jami’an tsaro da kada su yi barazana ga masu zanga-zangar domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba su ƴancin yin zanga-zangar lumana.
Solomon Dalung, wanda ya yi minista gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2019, ya yi nuni da cewa ƴan Najeriya na matuƙar shan wuya.











